Luke 16

1Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Akwai wani mai arziki da yake da wakili, sai aka yi karan sa da cewa wannan wakili yana fallasar masa da dukiya. 2Sai mai arziki ya kira shi ya ce masa, ‘Labarin me nake ji game da kai? Kawo lissafin wakilcin ka, don ba za ka sake zama wakili na ba.’

3Sai wakilin ya ce a ransa, ‘Kaka zan yi, da yake maigida na zai karbe wakilci daga hannuna? Gashi, ba ni da karfin noma ina kuwa jin kunya in yi roko. 4Na san abin da zan yi domin idan an fitar da ni daga wakilcin, mutane su karbe ni a gidajensu.

5Sai wakilin ya kira kowanne daya da maigidansa ke bi bashi, yace wa na farkon, ‘Nawa maigida na yake bin ka?’ 6Ya ce, ‘Garwan mai dari.’ Sai ya ce masa, ‘Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubuta hamsin.’ 7Ya kuma ce wa wani, ‘Nawa ake binka?’ Ya ce, ‘Buhu dari na alkama.’ Ya ce masa, ‘Ga tarkardarka, ka rubuta tamanin.’

8Sai maigida ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ‘ya’yan zamanin nan a ma’ammalar su da mutanen zamaninsu sun fi ‘ya’yan haske wayo. 9Ina gaya maku ku yi abuta ta dukiya ta rashin gaskiya, saboda idan ya kare, su karbe ku a gidaje masu dauwama.

10Wanda yake da aminci a karamin abu, mai aminci ne a babban abu, wanda yake marar gaskiya a karamin abu, marar gaskiya ne a babban abu. 11Idan fa ba ku yi aminci da dukiya mara adalci ba, wa zai amince maku da dukiya ta gaskiya? 12Idan kuma ba ku yi aminci da kudin wani ba, wa zai ba ku kudin da ke naku?

13Ba bawan da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ki daya, ya so daya ko kuwa ya amince wa dayan, ya raina dayan. Ba za ku iya bauta wa Allah ku kuma bauta wa dukiya ba.”

14Da Farisawa da ke da kaunar kudi suka ji dukan wadannan abubuwa, suka yi masa ba’a. 15Sai ya ce masu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abin da mutane suke girmamawa kwarai abin kyama ne a gun Allah.

16Attaura da litattafan annabawa suna nan har zuwan Yahaya. Tun daga lokacin nan ake yin bisharar mulkin Allah, kowa kuma yana kokarin kutsawa zuwa cikinta. 17Duk da haka, zai fi sauki sama da kasa su shude, da ko digo daya na attaura ya shude.

18Duk wanda ya saki matansa ya auri wata ya aikata zina, kuma wanda ma ya auri sakakkiya ya aikata zina.

19Akwai wani mai arziki, mai sa tufafi na alfarma masu tsada yana shagalin sa kowace rana. 20Aka ajiye wani gajiyayye a kofarsa, mai suna liazaru wanda duk jikinsa miki ne, 21Shi kuwa yana marmarin ya koshi da barbashin da ke fadowa daga teburin mai arzikin nan har ma karnuka sukan zo suna lasar mikinsa.

22Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, malaiku kuma suka dauke shi suka kai shi wurin Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi, 23yana cikin hades yana shan azaba, sai ya daga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li’azaru a kirjinsa.

24Sai ya yi kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayi na, ka aiko Li’azaru ya tsoma dan yatsansa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.’

25Amma Ibrahim ya ce, ‘Yaro, ka tuna fa a zamanka na duniya ka sha duniyarka, ka kuma karba abubuwa masu kyau, amma Li’azaru kuma sai wahala. Amma yanzu dadi ake bashi a nan, kai kuwa kana shan azaba. 26Banda haka ma, akwai rami mai zurfi, domin wadanda suke son ketarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ketaro zuwa wurinmu daga can.’

27Sai mai arziki ya ce, ‘To ina rokonka, Baba Ibrahim, ka aike shi zuwa gidan mahaifina - 28domin ina da ‘yan’uwa maza biyar, ya je ya yi masu gargadi kada su ma su zo wurin azaban nan.’

29Amma Ibrahim ya ce, ‘Suna da Musa da annabawa; bari su saurare su.’ 30Sai mai arziki ya amsa, ‘A’a, Baba Ibrahim, idan wani daga cikin matattu ya je wurinsu, zasu tuba.’ Amma Ibrahim ya ce masa, ‘In dai har basu saurari Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su rinjayu ba.’”

31

Copyright information for HauULB